Appreciation of some selected Akilu Aliyu’s poems

NAZARI DA SHARHI A KAN WASU ZABABBUN WAKOKIN

NA

IBRAHIM TIJJANI ABDULLAHI

YANKE
Nazarin waka rubutacciya na nufin yin zurfin tunani da kuma kyakykyawan bincike kan waka. Domin bayyana irin sakon da wakar ke dauke das hi da yadda mawakin ya zuba waka da kuma tsarata. Haka kuma da yin bayani dangane da yadda mawaki ya yi amfani da salon sarrafa harshe a cikin waka.

GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya ba mu ikon kamala wannan gagarumin aiki na bincike. Tsira da aminci Allah su tabbata ga fiyayyen halitta, Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W)
Za mu yi amfani da wannan dama don mika godiya ta musamman ga shugabanmu kuma malaminmu. Wato Malam Ibrahim Garba Satatima, wanda shi ya jagoranci wannan aiki ta fuskar yin dukkan wasu gyare-gyare, bada shawarwari da kuma taimakwa da kayan aiki. Bias ga irin taimakon da ya yi mana, muke fatan Allah ya ya ci gaba da taimaka masa da kuma yi masa jagora a dukkan fannoninsa na rayuwa, amin.
Haka kuma ba za mu taba mantawa da malamanmu ban a Sashen Nazarin Harsen Nigeriya. Kamar su Malam Bello A Muhd da Malam Bashir Ibrahim da Malam Tijjani Salihi da Malam Bashir Fagged a Malam Abdullahi B. Muktar (H.O.D) da Malam Muammad Abdu D/iya da Malama Fauziyya da malama Asiya da Malama Azima. Muna fatan Allah ya yi masu jagora a rayuwarsu amin.
Haka kuma zamu yi amfani da wannan dama domin mu mika godiyarmu ga Mal. Kabiru (Redman) K.S.C.O.E. kumbotso wanda shima ya taimaka mana da shawarwari da kuma kayan aiki mun gode ALlahh ya saka da Alkhairi amin. Haka kuma muna godiya ga Adnan Hayatu game da irin taimakon da yabayar.
A karshe muna mika godiyarmu da dukkan wanda ya taimaka mana, kuma ba mu ambaci sunansa ba Allah ya saka da alkhairinsa, amin.

SADAUKARWA
Ni kam, na sadaukar da wannan aiki ga mahhaifina. Wato Alhaji Gambo Abdullahi Sumaila da kuma Amina Gambo Abdullahi. Bisa la’akari da yadda su ka yi ta yin dawainiya da ni har, na kawo ga matsayin da nake a yanzu. Allah ya saka musu da alkairinsa amin.
Haka kuma ina fatan wannan aiki ya zama sadaukarwa ga malamaina da abokai da yayye da kuma `yanuwana baki daya
Rabi’u Garba (Falke)
Ni na sadaukar da wannan aiki ga iyayena da malamaina da kuma `yan`uwana dalibai musamman masu Nazarin Harshen Hausa da kuma abokiyar karatuna wato Aisha Gambo wadda Allah ya yi wa rasuwa. Da da kanin mahaifina Marigayi Alhaji Muhammadu (Kyauta) Allah ya gafarta musu amin.
Halima Muammad
Na sadaukar da wannna aiki ga iyaye na Alhaji Tijjani Abdullahi da Hajiya Rabi wada da kuma kanwata Safiya Tijjani (Ummi) da maigidana Alhhaji Tijjani Zawiya (Malam) da Maryam Tijjani Shu’aibu Koki.
Ibrahim T. Abdullahi
Na sadaukar da wannan aiki ga iyayenmu wadanda suke rayed a wadanda suka riga mu gidan gaskiya da fatan Allah ya ji kansu da rahama baki daya amin.
Zainab Mani `Yangora.
Wannan aiki zan sadaukar das hi ne ga mahaifina Alh. Sehu Mud Satatima. Allah ya ji kansa ya gafarta masa mu kuma ya kyautata na mu karsen amin.
Usman S. Ahmad
GABATARWA
Muna godiya ga Allah (S.W.A) wanda ya bamu ikon gabatar da wannan aiki. Tsira da aminci su tabbata ga manzon rahama Annabi Muammad (S.A.W)
Wannan aiki da muka gudanar aiki ne day a bayyana irin gudunmuwar da marigayi akilu aliyu ya bayar, musamman a fagen rubutattun wakokin Hausa. Domin wannan aiki na bincike ya yi bayani dangane da tarihin Akilu Aliyu da kuma bayani akan hanyoyin da ake bi wajen nazarin rubutacciyar waka. Sannan kuma an yi nazari da sarhi akan wasu zababbun wakokin Marigayi Akilu Aliyu wato wakar Kadaura da wakar Sako a Hannun Mumini da kuma wakar Dan-Daudu.
Haka kuma wannan aiki namu muna yi masa fatan ya kasance mai amfani ga al’umar hausawa da duk wani maijin harshen hausa da kuma uwa-uba almajirai masu nazarin hausa.
Daga karshe muna masu neman gafara dangane da irin kura-kurai da makamantansu da za a iya cinkaro da su.

ABUBUWAN DA KE CIKI
Bayanan share fage:
Shafin amincewa i
Yanke ii
Godiya iii
Sadaukarwa iv
Gabatarwa v
Kunshiya vi
Babi Na Daya
– gabatarwa 1
Dalilin bincike 1
Manufar bincike 1
Gudunmuwar bincike 2
Anyoyin gudanar da bincike 2
Farfajiyar bincike 2
Bitar aiyukan baya 3
Babi Na Biyu
Takaitaccen Tarhin Marigayi Akilu Aliyu Da Gudunmuwarsa A Fannin Rubutattun Wakokin Hausa.
– Gabatarwa 4
Takaitaccen tariin Akilu Aliyu 4
Rabe-Raben wakokin marigayi Akilu Aliyu 5
Wakokin Addini 7
Wakokin siyasa 7
Wakokin fadakarwa 8
Wakokin ilmi 8
Babi Na Uku
Hanyoyin Nazarin Rubutattun Wakoki, Nazari da Sharhi a Kan Wkaar ilmi ta “Kadaura”.
– Gabatarwa 9
– Hanyoyin Nazayin Rubutacciyar Waka 9
– Nazarin A kan wakar kadaura 11
– Jigon waka da warwararsa 12
– Yawa da tsarin waka 14
– Yawa baiti da yanayin dango da baiti 14
– Yanayin ma’ana a baiti 15
– salo da sarrafa harshe a cikin waka 15
– Amsa-Amo 15
– Farawa da rufewa 16
– Amfani da Karin harshe da sauran harsuna 16
– Amfani da kalmomi da jimloli 16
– Adaftawa 17
– Shari a kan jigon wkar kadaura 18
– Sharhi a kan salo da sarrafa harse 18
– Sharhi a kan zubi da tsari 19
Babi Na Hudu
Nazari da sharhi a kan wakar addini a “sako a hannu mumini”.
Gabatarwa 20
Nazari a kan wakar kadaura 20
Jigon waka da warwararsa 20
Zubi da tsarin waka 23
Yawan Baiti da yanayin dago da baiti 24
Yanayin ma’ana a baiti 24
Salo da sarrafa harshe a cikin waka 24
Amsa-Amo 25
Farawa da Rufewa 25
Amfani da Karin harse da sauran harsuna 26
Amfani da kalmomi da jimloli 26
Adaftarwa 26
Sharhi a kan jigon wakar kadaura 27
Shari a kan salo da sarrafa harshe 27
Sharhi a kan zubi da tsari 28
Babi Na Biyar
Nazari da sharhi a kan wakar fadakarwa ta “Dandauda”.
– Gabatarwa 29
Nazari a kan wakar dandaudu 29
Jigon waka da warwararsa 29
Zubi da tsarin waka 31
Yawan baiti da yanayin dago da baiti 32
Yanayin ma’ana a baiti 32
Salo da sarrafa harshe a cikin waka 32
Amsa-Amo 32
Faraway da rufewa 33
Amfani da Karin harshe da sauran harsuna 33
Amfani da kalmomi da jimloli 34
Adaftarwa 34
Sharhi a kan jigon wakar dandaudu 35
Sharhi a kan salo da sarrafa harshe 35
Sharhi a kan zubi da tsari 36
Sakamakon bincike 36
Sawarwari 37
Kammalawa 37
Manazarta 38
Rataye 39
BABI NA DAYA
Manufar Da Hanyoyin Gudanar Da Bincike
Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) day a bamu dammar rubuta wannan kundi na bincike. Bayan haka, a wannan babi an tabo abubuwa guda shida (6). Kamar yadda suke a tsarin kundin bincike. Wadannan abubuwa su ne dalilin bincike, da manufar bincike, inda a karshe zamuyi bitar ayyukan baya. Kuma za a yi bayaninsu daya-bayan-daya, kamar yadda suke cikin tsarin kundin bincike.
Dalilin Bincike
A zahirin gaskiya idan aka duba irin muhimmancin da rubutattun wakokin Hausa suke da shi.musamman wake-wake irin na marigayi Akilu Aliyu wanda suke da matukar amfani a tsarin rayuwarmu ta yanzu. Shine mukaga ya dace mu yi nazari a kan wadannan wake-wake domin kara fito da sakon da suke dauke da si a fili. Haka kuma dalibai `yan baya masu nazarin harshen Hausa za su sami sauki wajen nazarin irin wadannan wake-wake.
Bugu da kari, wannan aiki yana daga irin aiyukan da muke domin samunsaidar malanta ta kasa wato N.C.E.
Manufar Bincike.
Kadan daga cikin manufar wannan bincike shine, Binciko irin gudunmawar da marigayi Akilu Aliyu ya bayar, wajen bunkasa adabin Hausa. Kuma yana daga cikin manufar wannan bincike ya binciko rabe-raben jigogin wakokin Marigayi kamar haka, Addini, Ilimi, Siyasa da fadakarwa. Idan akayi la’akari da yadda aka sami sunayen jigogin wake-waken marigayi Akilu Aliyu za a gane cewa fito da wadannan abubuwa yana da matukar muhimmanci, kuma si ne manufarmu ga wannan bincike.
Gudunmwar Bincike.
Kamar yadda muka rigaya muka sani a duk lokacin da aka yi wani bincike to, wannan bincike, ba kamar gudunmawa zai bayar ba, musamman domin warware wata matsala ko, kawo sabon ilmi cikin al’umma da cigaba ta fuskar kere-kere da sauransu. To, wannan bincike namu yana da tasa gudunmawar, ta samar da wnai sabon ilmi cikin al’umma da kuma, bad a gudunmawa wajen bunkasa harsen Hausa.
Hanyoyin Gudanar Da Bincike
Domin samun nasarar wannan aiki namu akwai hanyoyin gudanar da bincike guda biyu da aka tsara.
Hanya ta farko it ace, karatun littattafai da mukalu da jaridu, da mujallu da kundayen bincike da suke da alaka da aikin da aka aiwatar. Hanya ta biyu da aka yi mafani da ita wajen samun bayanai ita ce: Tattaunawa ko ganawa baka dab aka da wasu malamai da dalibai masana adabin Hausa domin samun shawarwari da kuma Karin bayani. Haka kuma an gana da iyalin marigayi Akilu Aliyu.
Farfajiya da Iyakancewar Bincike.
Kamar yadda aka yi bayani tun a baya. Lallai wannan bincike zai tsaya ne, kawai ga nazarin rubutattun wakokin marigayi Akilu Aliyu. Wadanda jigoginsu ya shafi addini da ilimi da fadakarwa. Kuma zamu dauki waka dai-dai a cikin kowanne jigo domn yin nazarinta. Daga ciki akwai wakar ilmi mai taken “Kadaura Babban Inuwa” da wakar addini mai taken “Sako a Hannun Mumini” inda a karshe zamuyi nazarin wakar fadakarwa mai taken “Dandaudu”.
Wannan aiki zai takaita ne kawai a iya abubuwan da muka labarta a sama.
Bitar Ayyukan Baya/Ayyukan da Suka Gabata.
Binciken da aka yi an gano cewar ayni ayyuka da suke da laka da wanna aiki daga ciki akwai, nazarin wakar Hausa mai ban haushi cikin littafin Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare na Prof. Ibrahim Yaro Yahaya 1992.
Akwai sharhin wakar `Yan gagara wanda Shafi’u Akilu yayi a shekara 1994.
Bello A.A. da wasu (2001). Nazarin Wakar Sabo Tirken Wawa da Tahamisin `Yargagara. Kundin Binciken Samun takardar shauidar malanta ta kasa (N.C.E) A takaice wadannan su ne irin aiyukan da aka samu an gudanar kuma suke da alaka da wannan aiki.

BABI NA BIYU
Takaitaccen Tariin Akilu Aliyu Da Gudunmawarsa A Fannin Rubuttatun Wakokin Hausa
Gabatarwa.
A wannan babi an tabo muimman abubuwa da suka shafi takaitaccen tarihin marigayi Akilu, Salo da tsari da jigo da rabe-raben wakokinsa. Musamman irin rubuce-rubucen wakokinsa da suka danganci, addini da siyasa, da ilmi da fadakarwa. Kuma an kawo misali na wakoki daki-daki a karkashin kowane kaso, don fayyace abubuwa a fili da kuma samun saukin fahinta.
Takaitaccen Tarihin Akilu Aliyu.
Marigayi Akilu Aliyu dan asalin garin jega ne ta kasar Gwandu a Jahar Kebbi ta yanzu. An haife si a shekarar 1918. Ya fara karatun Alkurani awajen maaifinsa wanda aka fi sani da malam Aliyu Madaha saboda si ma’abocin ishiriniya ne. bayan rasuwarsa, a lokacin Malam Akilu yana dan shekara goma sha biyu (12) sai ya ci gaba da dauakr karatu wajen su Malam Tsao, Malam Ban Allah da Malam Mud Dantakusa. Da kuma wajen Malam Abdul’mumini inda ya fara karatun ilmi.
Malam Akilu Aliyu ya fara zuwa Kano don nemna ilimi, lokacin yana da shekaru goma sha biyar (15). Haka kuma neman ilmin ne ya kaishi ar Maiduguri (Borno) inda ya taba siyasa sosai a can. Daga baya ne Malam Akilu Aliyu ya dawo Kano da zama na din-dindin.
A kano babban malaminsa shine Mal. Mamud na Mal. Salga. A Kano Marigayi Akilu Aliyu ya zauna ya cigaba da koyo da kuma koyarwa tare da aiwatar da sana’arsa tag ado, wato dinki da kuma rubuce-rubucen wakoki har, ALla yayi masa rasuwa a shekarar 1999.
Batun rubuta waka kuwa, marigayi ya fara ne tun, yana yaro, kusan koyaushe a cikin kulla ta yake, har Allah ya yi masa rasuwa. Si kansa bai san iya adadin wakokinsa da ya rubuta ba. Saboda da yawa sun bace, amma bas u kasa dubu guda (1000) ba.
Rabe-raben Wakokin Malam Akilu Aliyu.
Gusau S.M. (1993) ya bayyana jigo da cewa “yana bayyana manufarko sakon da waka ke kunshe das hi, wanda ya hada tun daga farkonta harzuwa karshenta.
Bias la’akari da irin bayanai da suka gabata a iya cewa kowace waka tana da wata muhimmiyar manufa ko kuma sako da yake kunshe a cikinta. Wanda hakan shi ne yake a matsayin dalilin rubuta ta.
Saboda haka Malam Akilu Aliyu ya rubuta wakoki da dama, wadanda suke kunshhhe da sakonni iri daba-daban.
Haka kuma irin wadannan wake-wake suna taka muimmiyar rawa da kuma kyakykyawan wake-wake suna taka muimmiyar rawa da kuma kyakykyawan amfani cikin Al’umma a fannoni da dama. Musamman ta fuskar wayar da kan al’umma da fadakarwa da kuma uwa-uba wa’azantarwa ga jama’a.
Misali:- Wakar Kasaitaccen Gari Legas wadda take dauke da jigo ko sako na musamman da yake bayyana shahara ko kasaitar gairn Legas. Kamar yadda mawakin ya nuna cikin baitikan wakar.
Baiti na (1) sunan Allah kuddusu,
Saboda kiransa ne tabbas.
Baiti na (2) shi za na kira da in fara,
Wannan kuwa ya zama tilas.
Baiti na (3) na gaida da rasulu manzonsa,
Yau zan Magana akan Legas.
Baiti na (4) amma a takaice zan yi ta,
Don jin tsoron tsawon wakas.
Baiti na (5) aiki da yawa gabaninmu,
Zan tsakura dan batun Legas.
Baiti na (6) ilmi tafiya mabudinsa,
Domin haka ne na je Legas.
Baiti na (7) babban birnin Nigeira.
Kasaitaccen gari Legas.
Baiti na (8) kallo har ma yi ma more
Matukar mun je garin legas.
Baiti na (9) wani gun da abin da ke candin,
Amma wani sai garin Legas.
Baiti na (10) abu mai babbab da mamaki,
Jingim sike can garin Legas.
Baiti na (11) daga wanan sai kaje wancan,
Kullum a cikin garin Legas.
Baiti na (12) ikija da agege na leka,
Yayin da na je garin legas.
Baiti na (13) har mai wata fira 1-Yam-Ai,
Ta Apapa a can garin Legas.
Baiti na (1$) wannan gari fad a ban sha’awa.
Wane ne shi? Garin Legas.
Baiti na (15) tsoon kaya na tarihi,
An tattara cikin Legas.
Akwai wakokin marigayi akilu aliyu da dama wadanda suke da jigo na musamman sabanin irin wadanda aka saba gina waka kansu. Saboda aka anan, an yi kokarin takaita rabe-raben wakokin zuwa kaso hudu wato wakokin zuwa kaso hudu wato wakokin da jigonsu ya shafi addini da wakokin da suke dauke da jigo irin na siyasa da kuma masu dauke da jigon daya shafi fadakarwa da ilmi.
Wakokin Addini:
Malam Akilu Aliyu ya rubuta wakoki wadanda suke dauke da jigon addini ko abin day a shafi addini zalla. Misali:
Yau daren babbar salla.
Kamshin faida.
Aikin hajji ya wuce was.
Is’ra’I haske mai ganar da basira.
Sako a hannun mumini.
Wakokin siyasa
Marigayi Akilu Aliyu ya taba siyasa sosai a rayuwarsa. Hakan ne ma ya sa shi rubuta wakoki wadanda jigonsu ya shafi siyasa bias tsari da yanayi daba-daban. Daga cikin irin wadannan wake-wake a iya buga misali da wadannan
Ba maki Nepu sai wawa.
Baki uku sahariin NPC.
PRP rundunar nasara.
Wakokin Fadakarwa.
Kasancewar marigayi Akilu Aliyu malami ne shi kuma an san malamai akan ilimantarwa da kuma fadakarwa ga jama’a. marigayin ya rubuta wakoki bias tsarin jigon fadakarwa da dama. Misali:
`yan gagara
Duiniya rawar `yanmata.
Dan daudu
Itaciyar zumunta.
Dan gata.
Wakokin Ilmi
Malam Akilu Aliyu kamar yadda muka bayyana a cikin tarihin rayuwarsa, ya taso ne bias sha’awar neman ilmi ne ma ya kawo shin an Kano. Saboda haka, baa bin mamaki ba ne yadda ya rubuta wakoki wadanda suke dauke da bayanin muhimmancin ilmi. Misali:
Kadaura
Wakar kalubale
Ba wai wadannan rabe-raben su ne kadai irin rabe-raben wakokinsa ba. Akwai wasu nau’o’in wakokin da suke da jigogi daban da wadanda aka labarta a baya irin wadannan wakoki sun hadar da wakar B.B.C. da damina mai albarka da kasaitaccen gari Legas da Amsa ga wasika ta sha’irci da Daddadan Dadi Saniya da kuma wakar cuta ba mutuwa ba. Da dai sauransu.
Amma an takaita rabe-raben zuwa gida hudu domin samun saukin aiki da kuma fahimta ga maikaratu.

BABI NA UKU
NAZARI DA SHARHI A KAN WAKAR ILMI, MAI TAKEN “KADAURA BABBAR INUWA”.
GABATARWA
A wannan babi an yi nazari akan wakar, kadaura da bayani dalla-dalla gane da jigon wakar, bayani akan salo da sarrafa harshe da kuma zubi da tsarin wannan waka.
Haka kuma a bangare guda an yi sharhi a kan jigon wakar, zubi da tsari, da kuma salo da sarra harshe.
Muna fatan wannan zai kasance wata hanya ta bayyanar da irin sakon da kuma muimmanci da wannan wakar (kadaura) ke dashi.
Hanyoyin Nazarin Rubutacciyar Waka.
Kalmar nazari tana nufin yin zurfin tunani ko kuma zurfafa tunani ko jawabi na ilmi a kan wani aiki na adabi. Manazarci yana bayyana abubuwa guda hudu a wajen nazarin waka rubutacciya.
Bayanin sharer fage
Bayanin jigo
Bayanin zubi da tsarin
Bayanin salo da sarrafa arshe.
Bayanin sharer fage: Bayanin sharer fage ko gabatarwa, anan ana bukatar manazarchi ya yi bayanin asalin waka da tarihinta da sunanta da tarihin mawallafi wakar, sunansa da kuma shekar daya wallafa wakar, wadannan bayanai suna da muimmanci wajen ambaton sakon waka.
Bayanin jigo: Kowace waka tana da manufa ko sako wanda shine dalilin wallafarta. Haka kuma dukkan rubutacciyarwaka akan same tad a irin wannan manufa ko kuma salo. A nan mai nazari yana yin abubuwa guda biyu dangane da sakon waka.
Abu na farko da mainazari zai fara yi shi ne ambaton gundarin jigo na waka. Marubuta wakoki sun bambanta dangane da ambaton ainihin dalilin da yasa suka rubuta waka. Ana bukatar manazarci ya karanta waka yadda ya kamata. Domin wani lokaci marubuta sukan bayyana dalilin wakarsu, wani lokaci kuwa sai an yi karatu sosai za a iya tantance ainihin sakon da wuka ta kunsa.
Warwarar jigo: a nan manazarci zai dauki kowane baiti na waka ya yi sharhi na ciki da na waje ta hanyar bayyana ayoyin Alkur’ani, koHadisi ko zantukan malamai ko wasu abubuwa na rayuwa.
A wani lokaci ana samun baitoci masu yawa suna Magana akan abu guda daya. A wannan muhali sai manazarci ya tara baitocin ya yi mu su sharhi na bai daya.
Bayanin zubi da tsari: Zubi da tsari a wajen rubutacciyar wakar yana nufin yadda marubuci ya kulla carbin tunaninsa, ya rubuta su a cikin dango da baiti. Shi ma ana lura da abubuwa guda hudu (4) .
Tsari ko yanaytin dango da baiti na waka.
Yawan baiti.
Ambaton yanayin ma’ana a baiti.
Karin ma’ana.
Abinda da ake nufi da Karin ma’ana shi ne, idan waka tana da layikanta, sai aka fara mata wani layi a cikinta wannan shi ne Karin ma’ana. Misali sunayen layukan waka.
Layi na farko – Wa’awili
Layi na biyu – Tasnini
Layi na uku – Taslisi
Layi na hudu – Tarbi’i
Layi na biyar – Tahannisi.
Bayanin salo da sarrafa arshe: Salo zabi ne da marubuci yake das hi wajen rubutunsa. Wannan kuma, sine yake bambanta si da sauran mawaka, sarrafa harshe kuwa yana nufin yadda marubuci ya yi amfani da harsen Hausa wajen rubuta waka. A wannan mataki mai nazari yana yin abubuwa shida (6) Misali:
Duba yanayin ma’ana acikin baiti.
Duba yanayin kafiya ko amsa-amo.
Faraway da budewa a cikin waka.
Wasu marubuta sukan bude waka da yabo ko rufeta da yabon Annabi
Wasu marubutan kuma sukan fara waka ko su rufe da adireshinsu.
Wasu kuwa suna faraway ne kawai.
Amfani da kalmomi da jimloli.
Adaftarwa: Siffantawa, kamantawa, Babbantarwa, habaici, Karin Magana da sauransu.
Duba yadda marubuci ya yi amfani da Karin harshe da kuma sauran harsuna.
A takaice wadannan abubuwa da aka labarta sune abubuwan dubawa wajen yin nazarin rubutacciyar waka.
Nazari akan wakar kadaura: kamar yadda mukayi bayani tun, da farko. Marigayi Akilu Aliyu shi ne ya rubuta wannan wakar da hannunsa cikin tsarin rubutu Hhausar ajami. Amma, malam Muhammad Dalhatu na Jami;ar Ahmadu Bello Zaria, Shi ne wanda ya yi kokarin tattara wasu daga cikin wakokin marigayi Akilu Aliyu don rubuta su cikin hausar book, wanda hakan ya hadar ar, da wannan waka ta “Kadaura”.
Gundura jigon wakar kadaura.
Wannan waka jigonta kocokan yana nuna muimmancin ilmi. A takaice dai babbabn sakon da wannan waka ke dauke das hi, shi ne wayar da kan jama’a da kuma fadakar das u game da muimmancin ilmi. Haka kuma akwai zaburarwa ga jama’a game da neman ilmi kamar yadda ya nuna cikin wadannan baitoci masu zuwa a kasa.
Baiti na (6) a mazanmu ar matanmu yara da manya
Jama’a, mu san ilmi muna Tarawa.
Baiti na (7) shi ne kadaura, ilmi babbar gayya,
Inuwa mayalwaciya wajen hutawa.
Baiti na (11) shin ko akwai wani namu ba ilmi ba,
Mai kai mutum kokaluwar dorawa

Warwarar Jigo:-
Domin kara tabbatar da jigon wannan waka da kuma wasu `yan wannan jigogi, zai fi kyau mu shiga cikin wakar sosai ta hanyar zakulo wasu baitocin wakar domin yin bayani daki-daki a kansu.
Da farko dai mawakin ya fara bude wakarsa da sunan Alla a inda yake cewa.
Bai tin a (1): bismillahi das hi nake faraway.
Ko mai nake niyyar nufin faraway.
Sannan a baitinsa na biyu sai yayi gaisuwa ga Manzon Allah (S.A.W) da sahabbai da kuma ahlinsa baki daya.
Baiti na (2): na gaida Manzo Alu, su da abokai,
Mata, da `ya`yaye na ke tarawa.
Haka kuma a baiti na hudu (4) da na biyar (5) sai mawakin ya fara da jan hankalin jama’a game da irin sakon da yake san mikawa gas u Al’umma.
Baiti na (4): dan gargadine kwarya-kwarya zanyi,
Ba mai yawa ba kadan nake gutsurawa.
Baiti na (5): sannan na barku das hi ku dinga tunani.
Wato a kansa ku dai kuna komowa.
Haka kuma cikin baiti na 8, mawallafin yaci gaba da yadda ya kamata a ce jama’a sun dauki neman ilmi, wato suyi aiki tukuru da tsayawa ka’in da na’in game da neman ilmi, ba tare da nuna wata kasala ba ko lalaci.
Baiti na (8): lallai mu ja damara mu mike sosai.
Ba nuna lalaci da san gajiyawa.
A cikin baiti na 21 mawallafin wakar ya nuna cewar duk wani yaro maras ilmi ko kuma wanda bay a nemna ilmi to basi da wata mafita ko makama kyakykyawa a rayuwarsa.
Baiti na (21): yaro marar ilmi, tasono kenan.
Mai toshe hanci babu nunfasawa.
Haka zalika, a cikin baiti na 25, fadakarwa ce wannan marubuci ya yi game da amfanin ilmi ga mutum shi kansa, da kuma taimakawar ilmi wajen cigaban kasa baki daya. Lallai wannan baiti ya ja hankalin jama’a game da yadda za su nemi ilmi don taimakawa kasarsu da kuma su kansu.
Baiti na (25): ka yi kokarin neman sani don kanka,
Da kasarka aiki ne abin godewa.
Cikin baiti na 29, ar tambaya mawakin ya jefa ga jama’a, ind ayke tambayar wai ina amfanin jahilci, yana ganin gwanda mutuwa da zaman mutum cikin jailci. Hakan yana bayyana mana tsananin muni da jahilci ked a shi.
Baiti na (29): shin jahilci ransa mai ya dade ne.
Da zamansa dinnan gwamma macewa.
In maka sake natsuwaa cikin bitikan wakar zamu ga inda Malam Akilu Aliyu ya nuna cewa shi mai ilmi baya bukatar wasu kaya na kasaita ko kuma kudi domin nagartarsa ta ilmi da yake das hi ya fi jahili komai irin shigarsa ko kuma kudinsa. Wannan baiti ya kara fito da muhimmancin ilmi.
Baiti na (82): mai ilmi ko baida babbar riga,
Shi ne mafi Magana abar kamawa.
Cika makin baitin da za mu rufe dashi, shi ne baiti na 85, inda mawallafin yak e kara kira ga matasa dasu nemi ilmi, domin shi ne ado fiye da rigar sawa, domin jahilci da kayan kasaita shirme ne, kuma abu ne mai muni. Amma kuwa saurayi mai ilmi maras kayan ado, to, wannan shi ne abin kasaita cikin jama’a.
Wannan baiti ba karamin kalu-bale ba ne ga rayuwar matasa a yanzu. Domin yawancin jailan matasa su ne suka fi shiga arkar shaye-shaye da daba da kuma yadda ake amfani dasu wajen aikata miyagun laifuffuka cikin al’umma.
Saboda haka ilmi shi ne garkuwa ga dukkan wani matashi don samun kariya ga shiga mummunar rayuwa.
Baiti na (85) shi ne ado gun saurayi, ko yaushe,
Ko ya kasance bai da rigar sawa.
Zubi da tsari.
Kamar yadda aka yi bayani tun da farko, zubi da tsari a rubutacciyar waka shine yadda marubuci ya tsara waka da kuma yadda ya jeranta tunaninsa a cikin baiti. Bias la’akari da wannan, za’a iya cewa, wannan waka ta kadaura tana da bakaye da sha’awa da kuma shiga zuci sosai. Ganin yadda wannan mawaki ya tsara baitikan wakar daki-daki. Kuma kowane baiti yana kara wata ma’ana ne a cikin wakar.
Yawan baiti da yanayin Dango da kuma Baiti.
Wannan waka tana da baituka ar guda tamanin da bakwai (87).
Yanayin dango da baitin wakar kuwa shine, wakar dai iyar tagwaice. Wato tana da kwar biyu. Kusan kowane layi zai iya zama da gindinsa. Amma wasu layukan sukan zama lallai sai an hada layuka biyu sanna sub a da ma’ana.
Wani abin lura anan shi ne, wannan waka bat a da tsarin nan na sabi-zarce ko shangangara. Wato da datsa wata kalma ko rukunin wasu kalmomi gida biyu. A bar rabinsu a layi na farko, rabin kuma akai layi na biyu.
Yanayin ma’ana a baiti: Kusan kowane baiti yana iya bayar da cikakkiyar ma’ana. Amma wasu baitikan sukan yi farin bayani ne akan abinda baitin day a gabace su ke yi.
Wani abin lura anan shi ne, wanna waka bata da Karin ma’ana ko tahanisi.
Salo da sarra harshe:
Yanayin Salo:- Wannan waka tana da salo sassauka, wadda baya bukatar wani Karin bayani ga maikaratu ko kuma mai saurare dangane da sakon da wakar ke dauke dashi. Domin a farkon wakar kai tsaye ya nunawa jama’a inda sakon wakar ya dosa. A baiti na hudu (4) da na biyar (5) janankali ya yi ga jama’a sai kuma a baiti na sida (6) ya bayyana abinda yake jan hankali akai. Misali:
Baiti na (6): amazan mu har matanmu, yara da manya,
Jama’a mu san ilmi muna Tarawa.
Wani abin lura anan shi ne wakar dauke take da ma’ana da kuma bayani game da muhimmancin ilmi daya bayan daya wato daki-daki.
Amsa-Amo:- Layi na farko a wannan wakar bashi da wani amsa-amo, tsayayye. Kowane layi yakan kare ne da hharuffa ko kalmomi daban-daban. Misali: wa, kai, yi, ni da sauransu.
Amma, layi na biyu yana da tsayayyen amsa-amo (kafiya) guda daya na “wa”. A takaice dai babban amsa-amo, (kafiya) na wakar shi ne “wa”.
Farawa da rufewa acikin waka:”
A wannan waka, mawallafin ya bude wakarsa da sunan Allah da kuma yabon manzon Allah. Misali:
Bt na (1): bismillahi das hi nake faraway;
Ko me nake niyar nufin shiryawa.
Bt na (2): na gaida manzo Alu, su da abokai.
Matan da `ya`yaye nake Tarawa.
Hhaka kuma mawakin ya yio amfani da salon rufewannan na rufewa da adreshi wanda yake cewa
Bt na (87): ni ne mawakin nan na kofar wambai,
A kano, Akilu Aliyu mai tsarawa.
Amfani da Karin harshe da sauran harsuna:
Karin harshen da marubucin wannan waka ya yi amfani da si, Karin harshe ne irin na dai-daicciyar Hausa. Haka kuma marubucin wakar ya yi kokarin yin amfani da kalmomi na Hausa zalla. Amma da yake ba a rasa nono a riga, akwai wasu `yan kalmomi da mawakin ya yi amfani kodai daga harsen Larabci ko Turanci. Misali:
Larabci: Bismillahi, Fa’ida, Gafala, HHasada, da sauransu.
Turanci: Rasda, Bigiman (Bigman), Reliwen (Railway), Di’o (D.O) da sauransu.
Amfani da kalmomi da jimloli: Marubucin ba safai yake amfani da kalmomi masu tsauri ba a cikin wannan waka. Hhaka kuma ba wasu jimloli masu tsauri cikin wakar. Amma, akwai wasu `yan kalmomi kamar, wayan (wayo), kasgi, kumusgi, buntuna, da dai sauransu. Irin wadannan kalmomi suna da tsaurin fahimta. A bangaren jimloli a kwai wasu masu dan tsari. Misali:
Bt na (31): tirkasi aikin ya fi karfin wasa.
Zan buntuna maka kyas ka san ta kararwa.
Wannan jimla ta layi na biyu inda mawakin ke cea.
“zan buntuna maka kyas ka san ta kararwa”.
A gaskiya jimlar tana dad an tsauri a wajen fahimta.
Adaftawa:- Akwai wurare da wannan mawaki yayi amfani da zantuka na azanci da hikima da fasaha cikin salo daban daban, kamar habaici, ba’a, siffantawa, kamantawa da sauransu, misali:
Karin Magana:
Bt na (32): Hauka da jahilci suna da zumunta;
Makusanciya, ta kukut marar ajayawa.
Anan mawakin ya yi amfani da salon Karin Magana na “jahilci yafi hauka”

Habaici:-
Bt na (55): Ba za ka zam wani babba mai aiki ba,
Sai dai kurum a kira ka mai kutsawa.
Bt na (56): In anyi ma lakabi da mai kutsawa,
Ka tuna akwai wani lokacin makalewa.
Bt na (57): In kayi kutsin ma, ba ka zarce ba,
Wannan rawar kuwa gara kin takawa.
Karangiya:-
Bt na (14): Taro kacinci kacinci ko a cinta,
Wacce ce kazamar rayuwa mara yalwa?
Bt na (15): Kan-ta-kalai gashe babu mai ko naso,
Dafe babu room ko na dan lasawa.
Ba’a:-
Bt na (21): Yaro marar ilmi tasono kenan,
Mai toshe anci babu nunfashhi.
Kamantawa:-
Bt na (51): si jahili, kun ganshi, shi ne hoto,
Tamkar baka ba tsirkiyar daurawa.
Bt na (52): Ba na zaton zai fa’ida ga mahharbi,
Tamkar tukunya wacce ba toywa.
Bt na (53): In ba a gasa tab a, tai rakaukau din nan,
Kunsan ruwa a cikinta bai zaunawa.
Sharhi akan jigo:-
Wakar kadaura tana daya daga cikin wakokin Akilu Aliyu da akan rera a gidajen radiyo. Wannan waka dai mawakin yana kokarin jawo hankalin jama’a ne domin su dage kan neman ilmi.
Babbar manufar wannan waka itace don muimmancin ilmi. Akilu Aliyu yana ganin neman ilmi ba karamin abu ba ne a rayuwa.
Idan aka yi la’akari da irin hujjojin day a kawo wanda yake nuna wa jama’a cea ba wani abu da mutum zai zama ko ya samu ba tare da ilmii ba, kuma ya nuna cewa da rayuwar jahili gara mutuwarsa. Inda yake kira ga jama’a lallai su dage su kuma zabura kan neman ilmi ba tare da wata kwana-kwana ba. Misali:
Bt na (41): Jama’a mu zabura ba kwana, ba lauje,
Allahh ya bamu muwafukar dacewa.
Sharhi akan salo da sarrafa harse:-
Fitaccen salon wannan waka shi ne yadda wannan mawaki yake amfani da kalmomi wajen dunkule zance gu guda, da kuma yadda yayi amfani da baitika a jere yana mai zayyana irin aiyukan dab a za su yu ba jahili ya yi. Wato sai a dai mai ilmi, wannan baiyuka kuwa sun fara ne tun daga baiti na 58,59,60,61,62,63,64,65,66,67,68,69,70,71, cikin wadannan baituka ne mawakin ya yi ta zayyana irin aiyukan da lallai sai mai ilmi a ke bukata, ba jahili ba. Haka kuma wani salon sarrafa harshe wanda mawakin ya yi amfani da kalmomin amsa-kama. Misali: Kankamba Bt 83, Wawa Bt 74; da rakakau, Bt 53; da dai sauransu.
Zubi da tsari:-
Wannan waka dai tana da tsarin layuka bibiyu ne, wato `yan tagwai. Kuma amsa-amon wakar yakan kare da “wa”. Wato a layi na biyu kenan. Aka kuma akan samu yawancin layukan sub a da ma’ana cikakkiya, amma wasu sai an hade layuka guda biyu ko fiye don fitar da ma’ana cikakkiya. Wani abin sha’awa. Shi ne adadin baitikan wannan waka guda 87, amma kuma mawakin ya isar da sako wanda yake cikakkene ga jama’a. wanda in rubuta shi za ai a zube to littafi guda za a yi.
SHAFI NA HUDU
Nazari da sharhi akan wakar addini sako a hannun mumini.
Gabatarwa
A wannan babi an yi nazari a kan wakar addini. Wato sako a Hannun Mumini, da kuma yin sharhi game da jigo, salo da sarrafa harshe da kuma zabi da tsarin wannan waka mai taken sako a hannun mumini, muna fatan nasarar wannan aiki.
Nazari akan wakar, sako a hannun mumini:-
Ita ma dai wannan waka marigayi AKilu Aliyu ne ya rubuta tad a hannunsa cikin Hausar ajami. Haka kuma wannan waka tananan a rubuce cikin fasaha a kiliyya wanda aka rubuta cikin Hausar boko a shekarar 1976.
Gungarin jigon, wakar sako a hannun mumini:-
Wannan waka jigonta dai bai wuce addini ba. Domin wakar gaba dayanta tana Magana ne akan ibada ta aikin hajji. Wannan ibada kuwa tana daya daga cikin shika-shikan musulunci biyar (5) wannan mawallafi ba wai yana koyar da yadda ake aiwatar da ibadar ba ne illa, yana nuna mana yadda ya dokanta da zuwa aikin hajji. Haka kuma akwai jan ankali ga al’umma ga dukkan wani mai hali da yayi kokarin zuwa aikin haji.
Kamar yadda ya nuna cikin wadannan baitika na kasa.
Baiti na (3): Ya alhazaya kun ga ni,
Dinbin bukata ce dani.
Baiti na (4): sai dai yawan rauni gare,
Ni, akwai rasin karfi a ni.
Baiti na (50): Bayau ba ne ma tun tuni,
Nika, son a je makatan da ni.
Baiti na (6): Raina sin a can tun tuni,
Nan ne jiki ya tsayar da ni.
Baiti na (28): Dukkan musulmi mumini,
Zai ce, ina ma dai da ni?
Baiti na (29): Nai addu’a dominku ni,
Ta gama da kowane mumini.
Warwarar jigon wakar sako a Hannun Mumini.
Kamar yadda bayani ya gabata tunda farko, babban jigon wannan waka dais hi ne bayani game da yadda shi wannan mawallafi ya dokanta da zuwa aikin hajji. Amma ba a rasa `yan kananan sakonni a cikinta, kuma za mu dan tsakuro wasu daga cikin domin yin bayani a kansu.
A baiti na farko, mawallafin ya bude wakarsa da nuna cewa skao ne yake da nufin baiwa alhazai. Kuma har ya shaide su da cewa za su kai wannan sako ba tare da wani nuku-nuku ba. Wannan kuma shi ne taken waken.
Baiti na (1): Sako a annun mumini,
Zai kais hi ba wani bambami.
Sannan kuma cikin baitinsa na biyu sai yace, yana kiran sunan Allah mahaliccinsa. Wanda hakan yake nuna neman tabarraki ne ga wannanwaka tasa.
Baiti na (2): ni na kira sarki gwani,
Wannan daya samar dani.
A baiti na 22 sai mawallafin ya nuna mana yadda yake ji in ya ji jirgin alhazai ya tasi. Anan ya nuna dokinsa fiye da yadda ya nuna cikin baiti na 5 da 6. Inda y ace duk lokacin day a ji tashin jigin sama, to, abin yana tayar masa da hankalinsa sosai.
Baiti na (22): Jirginku can da sike dirin,
Tashinsa ya rikitar da ni.
A baiti na 23 da 24 sai wannan mawallafi ya ci gaba da labarta mana yadda yake ji game da tashin Alazai. Inda yake cea.
Baiti na (23): ya daddaga mini hhankali,
Wayyo, ina ma dai da ni.
Baiti na (24): Ya dagula mini zuciya,
Kunanta ya kidimar da ni.
Whaka dai, wannan mawaki ya yi ta jero baitika wadanda suke cike da begen zuwa aikin haji, wanda ko da mai saurare ne ya ji si ma abin zai motsa shi, ya ji begen zuwa aikin hajin ya ratsa shi.
A wani baiti kuwa addu’a ce malam Akilu Aliyu ya yi wa maniyata. Inda yake yi musu fatan Allah ya kaisu lafiya ya kuma dawo da su lafiya.
Baiti na (29): Ni addu’a dominku ni,
Ta gama da kowane mumini.
Baiti na (30): Allah shi kai ku da lafiya,
Ya raba ya sarki gwani.
Baiti na (31): Ya rabba dawo da su,
Kuma, lafiya sutarar da ni.
Can in mun nitsa cikin wakar, mawallafin ya mika gaisuwarsa ta bankwana ga dukkan alazai. Da kuma nuna irin begensa na rabuwa das u wadannan Alhazai.
Baiti na (43): kuma rarrabarmu ta ku da ni,
Sha’anin shina rikitar dani,
Baiti na (44): Ya bani ciwon zuciya,
Miye yak e warkar da ni,
Baiti na (45): Sai saduwarmu ta ku dani,
Shi ne dawa’i magani.
Zamu gani daban a wani haitin inda shi Akilu Aliyu yake nuna mana cewa ciwon nasa ba wai ya warke duka ba ne, a’a, har, sai ya samu dammar zuwa can kasa mai tsarki ya ziyarci Manzon Allah (S.A.W).
Baiti na (47): Ban an kadai ta takaita ba,
Karin bayani ne da ni.
Baiti na (48): In je madina garin muhamman,
Madu ne sahihin magani.
Baiti na (49): In durkusa in gaida shi,
Na san shina amsa wa ni.
A karshen wannan waka ta Akilu Aliyu, kokarin mika gaisuwa ya yi da kuma yabo ga fiyayyen halitta, wato Annabi Muhammadu (S.A.W).
Haka kuma ya yi gaisuwa ga sahabbai da ahlin gidan Annabi (S.A.W). wanda kuma wannan shi ne a matsayin murfin wannan waka.
Baiti na (54): na gaida maulana Muham.
Madu dai da jakada mumini.
Baiti na (55): Tsira, amincin rabbana,
Su yawaita kowane zamani.
Baiti na (56) A gare shi, har abada kuwa,
Matukar korewar zamani.
Baiti na (57): Matansa `ya`yayensa, A-,
Lu, saabu, na gaishe ku ni.
Zubi da tsari.
Bisa la’akari da yadda aka zuba baitukan wannan waka da kuma tsarin ma’ana, wadda ked a saurin jan Hankali ga mai kartu ko saurare. A iya cewa wannan waka tana da wai kyakykyawan tsari mai ban sha’awa. Haka kuma, baitukan wakar suna cikin tsarin rerawa tare da bayani dalla-dalla.
Yawan baiti da yanayin dago dana baiti.
Baitin wannan waka ya kai har guda hamisn da bakwai (57).
Yawan dango da baitikan waka. Wannan waka dia iyan tagwai ce (kwar biyu). Aka kuma ba dukkan dango ne ke iya tsayawa da gindinsa ba. Wato wasu layukan sukan zama lallai sai an ha su, su biyu sannan su bayar da ma’ana. Amma, wasu layukan sukan tsaya da kafafunsu don bad a ma’ana cikakkiya.
Akwai wasu layukan da aka yi amfani da tsarin nan da datsa kalma daga layin farko a kaita layi na biyu. Shangangara ko sabi zarce. Wanda hakan ne yasa wasu layukan bas u iya tsayawa da kafafunsu.
Misali:
Baiti na (33): Kuyi gaisuwa ga rasulu ka,
Kan alhasan, ku isar wani.
Baiti na (35): Na gaida maulana Muham,
Madu dai jakada, mumini.
Yanayin ma’ana a baiti.
Dukkan baitukan wannan waka suna bad a ma’ana cikakkiya. Aka kuma baitukan wannan waka an tsara su ne bias tarin bayani daki-daki.
Misali:-
Baiti na (9): Ya alhazaya, ku tuna da ni,
Gun addu’a, ku sigar dani.
Baiti na (10): A cikinta dan sarki gwani.
Allah shi sa ku fadar dani.
Baiti na (11): A safa da marwa tuninku ni,
Arfa ku aut a gami da ni.
Salo da sarrafa harshe.
Yanayin salo: Salon wannan waka sassauka ne. wato dai kai tsaye sakon wakar ke fitowa, kuma daki-daki. Mai karatu ko saurare ba ya
Bukatar wani Karin bayani, dangane da irin sakon da wakar ke dauke das hi.
Wannan mawaki bai sarkafa zantuka ko wasu kalmomi masu tsaurin fahimta ba. Tina baitikan farko na wakar ya fara bayyana irin sakon da yake son isarwa. Misali:

Baiti na (5): ba yau bane ma tun tuni,
Nika son a je makatan da ni.
Baiti na (6): Raina shin a can tun tuni,
Nan ne jiki ya tsayar da ni.
Farawa da rufewa:
A wannan waka Malam Akilu Aliyu yana fara budewa ne das hi kansa taken wannan waka. Amma, a baitinsa na biyu ya kawo sunan Allah. Sai dai wani abin lura si ne bai yi amfnai da salon nan na yabon Manzon Allah ba. Misali:
Baiti na (1): Sako a hannun mumini,
Zai kais hi ba wani bambami,
Baiti na (2): Na kira sarki gwani,
Wannan day a samar da ni.
Haka kuma mawakin ya rufe wakar tasa da yabon Manzon Allah tare da gaisuwa ga ahlinsa da kuma sahabbai na Manzon Allah (S.A.W). Misali:
Baiti na (51): Matansa `ya`yansa A-
Lu. Sahabu, na gaishe ku ni.
Amfani da Karin harshe da Sauran Harsuna.
Yawancin kalmomin da aka gina wannan waka das u, duk suna daga cikin Hausa daidaitacciya. Wato Karin harshen daya yi amfani das hi ya yi kokarin yin amfani da wanda yake daidaitacce ne. amma a kan samu wasu yan kalmomi nan da can, cikin wakar wadanda karinsu ya an banbanta da kari daidaitacce. Misali: kamnarka, shina, da sauransu.
Amma a bangaren amfani da kalmomin aro kuwa, mawakin ya yi amfani ne da `yan kalmomi kadan daga harshen larabci kuma in muka lura kwarai, aron nasu yakan zama wajibi ne misalign irin wadannan kalmomi: Allah, Rabbi, Arrasulu, Ta’ala, da sauransu. Wani abin lura anan shi ne babu wata cikakkiyar kalma da aka yi amfnai da ita daga harshe turanci.
Amfani da kalmomi da jimloli.
Wani abin sha’awa anan shi ne yadda mawakin ya kauracewa yin amfani da kalmomi masu tsauri ko kuma gina jimla mai tsaurin gaske. In kalmomin da za’a kira su tsaurara a cikin wakar bas u da yawa. Misali: Bimbimi, yankwaci.
Game da jimloli masu tsaurin fahimta su ma`yan kalilan ne, basu da yawa. Misali:
Baiti na (21): Ya alhazai tashinku ni,
Matuka ya jedantar da ni.
Wannan jimla ta layi na biyu tana dad an tsaurin fahimta. Wato inda yake cewa.
“Matuka ya jedantar da ni”.
Adaftawa.
Na safai mawakin ya yi amfani da kalmomi ko jimloli na zantukan azanci ko hikima na. watakila dan wakar tana dauke da jigon addini ne. domin an tsara wakar ne da nufin nuna shauki da begen mawakin na uwa aikin haji, saboda haka, ba wasu kalmomi na azanci ko hhakima sai. Da yake hausawa su ce “Ba a rasa Nono a Riga”. Misali: Karin Magana:-
Baiti na (27): Don ni Aliyu akwai-ya-ba-
Bu na zama wannan zamani.
Wannan baiti yana dauke da Karin Magana wanda hausawa sukan ce “Akwai ya babu”.

Sharhi a kan jigon wakar sako a hannun mumini:-
Wannan waka babban jigonta a kan addini ne. abubuwan da ta kunsa na addini za mu iya cewa nuna mahimmanci ne na aikin Haji da kuma jan hankalin al’umma game da aikin Haji, wato nuna musu muimmancinsa da kara sanyawa jama’a shauki na begen zuwa aikin Haji.
Kusan tun, a baiti na 3 ar zuwa baiti na 53 mawakin yana ta yin bayani ne game da sakonsa day a ke son baiwa Alhhazai da kuma irin yadda yake ji game da rashin samun dama ta zuwa aikin haji. Bugu da kari kuma, mawakin ya yi amfani da wasu baituka don yin bayani game da wasu rukunan aikin hhaji. Wato tun, daga kan dawafi, jifan sahidan, da hawa arfa da kuma safa da marwa.
Hhaka zuwa kan baiti na 57, gaisuwa ce mawakin ya yi ga Manzonn Alla da Ahalinsa da Sahabbansa.
Sharhi Akan Salo Da Sarrafa Harshe.
Dangane da salon sarrafa harshe, mawakin ya bayyana sakon da yake so ya isar cikin harshe mai sauki. Ko da yake dai akwai kalmomi na kai, amma, basu taka-kara sun karya ba. Wato bas u da yawa sosai. Kila domin wakar na dauke da jigo na addini ne shi yasa mawakin sassarko kalmomi irin na azanzi a wakar ba. Wannan si yasa wakar da tafi sa-sakai. Amma duk da haka akwai habaici dad a kamance a baiti na 27 da baiti na 42.
Sharhi a kan zubi da tsari:
Tsarin wakar yana da ban sha’awa kuma an nuna basira kwarai. Wakar dai tana da kyar biyu ne, haka kuma asma-amo wakar guda daya ne “ni”. Abin lura anan shi ne yadda mawallafin ya tsara wakar ikin ‘yan baitika kadan da basu wuce 54. Amma kuma suke cike da bayanai masu gamsarwa.
BABI NA BIYAR
Nazari Da Sharhi Akan Wakar Fadakar Dandaudu.
Gabatarwa
A wannan babi na biyar an tabo abubuwa da dama wadanda suka shafi nazari da sharhi akan wakar Dandaudu. Sharhin kuwa ya ada da salon wakar da salo da sarrafa harshe da zubi da tsarin wakar, wadannan abubuwa da aka labarta su ne muimmai da aka yi bayani cikin wannan babi
Nazari Akan Wakar Dan Daudu.
Wannan waka tana daga cikin wakokin marigayi Akilu Aliyu wadanda ya rubutu su da nufin fadakarwa ga al’umma. Ita ma an rubutata cikin Hausar ajami aka kuma, tana nan rubuce cikin littafan fusaha kiliyya wanda aka buga a shekarar 1976.
Nazari Akan Wakar Dan Daudu.
Babban sakon da wannan waka ke dauke das hi, bai wuce dakarwa ba game da illar da ke tattare da dabi’ar nan ta Daudanci (Dandaudu). Zamu faimci haka tun a baitin farko wannan waka da ta baiti na biyu, inda kai tsaye mawakin ya dira kan wannn dabi’a. ke nuna irin kaskancin wannan dabi’a ta Daudu.
Baiti na (1): Af jama’a ku bari in waigo,
In taba dan rakiyar tamakwalla.
Baiti na (2): Danhamsin yake ko Dandaudu?
Wa ma zai kula garar kasha.
Warwarar Jigo:-
In muka duba cikin baitikan wannan waka, tun a farko mawallafin fara yin bayani ame da Dandaudu. Haka kuma baiyi wata-wata sai ya zaiyana mana irin hasarar da dandaudu ya yi a rayuwarsa. Domin ya nuna Dandaudu a matsayin wanda ya yi batan-bakatantan. Wato bas hi ga suntsu kuma bas hi ga tarko. A ganin wannan mawaki, Dandaudu ya baro maza ne kuma ba zai kai ga mata ba.
Baiti na (6): Ba sia tsuntsu, ba si dabba,
Jamage shi ke, mai ban hausi.
Baiti na (7): Babu fikafikai gun dabba,
Tsintsu shi kuwa bas hi hakori.
A wannan baiti kuma sai mawallafin ya nuna yadda Dandaudu ya yi watsi da girma da daraja wacce Allah ya yi masa ta fifiko fiye da mata. Wato yafi so ya koma kamar mace, wacce kasansa take a daraja.
Baiti na (9): ya ki mafi girman daraja tasa,
Shi ya zabi ta karshen baya.
Haka kuma a wani baitin mawallafin ya bayyana kiyayyarsa ga masu dabi’ar nan ta daudanci inda ya kara karfafa kiyayyarsa da nuna hana cewa baya kaunar mai kaunar Dandaudu.
Baiti na (14): ban a son Dandaudu hakika,
Mai sha’awa tasa shi ma na ki.
Saboda yadda wannan mawakin ke kin Dandaudu har, la’ana ya yi ga masu wannan dabi’a ta daudanci ya kuma bayyana shi da cewa dai-dai yake da a yanka si saboda irin barnarsa cikin al’umma.
Baiti na (16): Allah ma wadaran Dandaudu,
Zin diki shike dai-dai yanka.
Baiti na (17): Bas hi da airi sai tula sharri,
Gara a kar matsiyacin banza.
Bugu da kari wannan mawallafi ya nuna illar Dandaudu da cewa ta fit a barowa. Saboda irin ayyukansa na barna da dabi;unsa na rashin mutunci.
Baiti na (20): gara ba awo ma da na daudu,
Mai a karairaya zaren mata.

A wani baitin sai kuma mawallafin ya nuna mana yadda uban Dandaudu ya yi hhasara har ubi biyu. Wato bayan an yanka ragon suna aka yi rashin sa’a, day a zama lalatacce.
Baiti na (32): Gad a ua za,a lalatacce,
Bayan an kasha ragon suna.
Malan Akilu Aliyu ya bayyana uban Dandaudu da cewa kullum yana cikin takaici domin dansa bas hi da wani amfani a rayuwa.
Baiti na (25): har abada ba huce takaici,
Tare da Daudu, uban `yan banza.
Anan kuma mawallafin ya rufe wakarsa da cewa. Allah ya tsare kansa da shiga Daudanci, inda yake ganin gwamma wannan dan nasa a ya zama gyartai. In kuma hakan bata samu ba, to gara ya mutu a huta daya.
Baiti na (32): Ni da ace dana zama shi,
Gara ace mini ya zama gyartai.
Baiti na (33): Ai day a zam Dandaudu jinni na,
Gara ya zam ajali ya sauko.
Zubi da tsari:-
Wannan waka ta Dandaudu tana da wani irin tsari mai birgewa ga a jama’a ko dai maikaratu ko ga mai sauraron wannan waka. Dalili kuwa ce, wakar tana cikin wani yanayi na kyakykyawan tsari. Ta yadda mai karatu ko mai saurare zai fahimci sakon kai tsaye. Wanna wakar kanta suna jere ne daki-daki tun daga kan bayani game da kowane ne Dandaudu. Da kuma irin Dabi’unsa, ko alayensa har, zuwa kan irin da mahaifan Dandaudu suka yi. Kuma dukkan abitikan suna biye daya-bayan daya.
Yawan baiti da yanayin Dango da na Baiti.
Wannan waka tana da baitika da suka kai har, guda talatin da hudu (34).
Yanayin dango da baiti. Kamar sauran wakokin da aka yi nazarin su a baya, ita ma wannan waka iyar tagwai ce. Wato mai kwar biyu. Aka kuma, yawancin layukanta sukan iya tsayawa da kafafunsu. Amma akwai wasu layukan da sukan karasa ma’anar abinda aka zayyana alayi na farko.
Haka kuma ko kadan mawakin bai yi amfani da tsarin sabi-zarce ko sangangara ba.
Yanayin ma’ana a baiti:
Tsarin baitikan wannan waka suna da ban sha’awa. Domin kowane baiti yana iya bad a ma’ana cikakkiya. Haka kuma, baitikan suna bayani daki-daki. Wato dai baiti ma biyu na biyu yana Karin bayani ne akan baiti na farko.
Wani ain lura shi ne wannan waka bat a da Karin ma’ana (Tahamisi).
Salo da sarrafa harshe.
Yanayin salo:- Salon da mawakin ya yi amfani das hi salo ne mai karashi, kuma mai saukin fahima.
Dalilin da yasa hakan kuwa shi ne, mawakin ya saka zantuka na azanci da hikima don jan hankalin jama’a. aka kuma ya bayyana sakonsa cikin wannan waka a fili. Ba tare da boye ma’a nab a. kuma kai tsaye yake bayyana irin sakon da wakar ke dauke dashi.
Amsa-Amo:- Wannan waka bat a da salon nan na tsayayyen Amsa-amo. Wato layi na farko bashi da wani tartibin amsa-amo (kafiya). haka kuma shi ma layi na biyu bas hi da wani tsayayyen amsa-amo.
A takaice dai kowane layi, na farko da na biyu na wannan waka bas hi da tsayayyen amsa-amo (kafiya). Kowane layi yakan kare da kowace irin kalma ko harafi. Misali: sa, ki, shi, ki, da sauransu.

Farawa da rufewa:- kamar yadda aka sani cewa wasu mawakan sukan bude waka da adireshinsu ko kuma yabon Manzon Allah. Amma ita wannan waka tsarinta ba aka bane, don kuwa an bud eta ne kai tsaye bias ga gundairn sakon da mawakin ke son isarwa. Misali:
Bt: 1. Af, Jama’a ku bari in waigo,
In, tabo dan rakiya ta-makwalla.
Haka kuma wannan waka an rufe tab a tare da yin salon nan na bayyana adreshi ko yabon Manzon Allah ba. Don kuwa mawakin ya rufe wakarsa ne da bayanai cikin baiti wanda ke nuna kiyayyarsa ga Dandaudu inda yake nuna da dai ace dansa ya zama Dandaudu to, gara a dannan nasa ya rasu. Misali:
Baiti na (34): Ai’wallai da dai ya yi ni dai,
Gara ya mutu, shi yafi sauki.
Amfani da Karin harshe da sauran harsuna:
Mawakin ya yi amfani ne da Karin harshe irin na daidai tatacciyar Hausa. Haka kuma, koda kalmomin da aka yi mafani das u yawancinsu a cikin Karin harse na daidaitacciyar Hausa. A dangane da amfani da kalmomi wadanda suke an aro su ne daga sauran harsuna su ma wadannan bas u da yawa. Misali: kala’I, kaddara, ta’ala, Allah, zindiki, Allahi da dai sauransu. Wani abin sha’awa shi ne ba wata kalma wacce kai tsaye za a ce an aro tane daga harsen turanci kuma aka yi amfani da ita cikin wannan waka.
Amfani da kalmomi da jimloli:-
A gaskiya wnnan waka bata dauke da wasu kalmomi masu tsauri, aka kuma, ba irin jimloli masu arshen damo ko kuma tsaurin fahimta. A takaice dai, a iya cewa kalmomn da aka gina jimloli das u da kuma irin jimlolin da aka gina wakar dasu duk ba masu rikitarwa ba ne ko kuma saurin fahimta.

Adaftarwa:- wannan waka tana cike da kalmomi masu nuna hikima da azanci. Kamar, habaici, Karin Magana, ba’a da sauransu. Amma anan an tsakuro wasu daga cikin irin wadannan zantuka na azanci domin buga misali.
Karin Magana.
Baiti na (6): Bas hi a tsuntsu bas hi a dabba,
Jemage si ke mai ban haushi
Wannan abiti yana dauke da irin Karin maganar nan na hausawa wanda ake cewa “bas hi ga tsuntsu bag a dabba”. To amma mawakin ya juya wata kalama ne domin baitin ya tashi sosai ya kuma fitar da ma’ana cikakkiya.
Zambo:-
Baiti na (17): Bas hi da airi sai tula sharri,
Gara a kar matsayacin banza.
Baiti na (18): Ko ba a karshi ba gara a daure,
Har abada a kaso ar kullum.
Habaici:-
Baiti na (3): Domin in nuna si a fili,
Har ma ai masa kallon banza.
Baiti na (4); can wani sashashan daga gefe,
Wofin wofiyo banzar banza.
Siffantawa:-
Baiti na (8): Si dai ya zama jakin-dokin,
Ya bata wa mazaje suna.
Ba’a:-
Baiti na (9): Ya ki mafi girman daraja tasa,
Shi ya zabi ta karshen baya.
Baiti na (13): Ya ki rabon da ta’ala yai yi,
Ya bujire wa umarnin sarki.
Sharhin akan jigon wakar Dandaudu:-
Wannan waka ta Dandaudu kusan a iya cewa kanwace ga wakar nan ta `yargagara. Babban jigon wannan waka shi ne fadakarwa ga al’umma game da illar dabi’ar daudanci.
A cikin wakar Akilu Aliyu yana ganin lalacewar duniya ta tabbata wurin Dandaudu. Haka kuma si a ra’ayinsa bai dace a bar Dandaudu aka kawai a gari ba, yana gani zaifi kyau a daure si a jarun da kuma jiki mai tsanani.
Mawakin bai tsaya anan bad a ya bayyana irin asarar da mahaifin Dandaudu ya yi. Aka zalika, mawakin ya rufe wakar sa ne da cewa da dai ace dansa ya shiga Daudu to gwamma wannan dan nasa ya mutu
Sharhi a kan salo da sarrafa arshe.
Ko da yake wannan waka bata da tsawo sosai. Wato duka-duka, yawan baitocinta guda 34, amma cike take da laffuza na gargadi da soratawa game da illar dabi’ar Dandaudu.
Da farkon faraway kamar ragowar wakokinsa na gargadi, a wannan waka Akilu Aliyu yayi amfani da sassaukar Hausa. Sannan kuma akwai ma’ana. Wato bayan ya bayyana Dandaudu sai kuma ya shiga bayyana irin dabi’unsa
Wani abin sha’awa a wannan wakar si ne irin yadda wannan mawaki ya yi amfani da zantukan azanci cikin waka.
Sharhi akan zubi da tsari:
Kamar yadda idan muka duba zamu gani, wannan waka na da tsarin layi bibiyu ne kowane baiti. Wato dai `yar tagwai”. Ke nan. Amma kuma baitikan, ko kuma layukan karshe na wakar baki daya kowane abin da yake karewa da si ya bambanta da na saura.
Haka kuma wani abin burgewa shi ne yadda aka tsara wakar cikin wani yanayi wanda kowane baiti da kuma layi ko kuma dango na iya bada ma’ana, amma akwai wasu `yan baitika da dango dake bukatar taimakon dan-uwansa kafin ya bada ma’ana.
Misali: 34: Ali wallahi da dai ya yi ni dai,
Gara ya ma mutu, si yafi sauki.
Sakamakon bincike:
Wannan bincike ya bayyana irin aikin da wani fitaccen mawaki kuma marubuci ya yi domin nusarwa da kuma fadakarwa da umartarwa ga jama’a.
Abubuwan da aka yi binciken a kansui su ne nazari da sharhin wasu wakoki guda uku (3). Wakar ilmi ta kadaura da wakar adinin wai taken sako a hannun mumini inda waka ta uku it ace wakar fadakarwa maitaken Dandudu.
Haka kuma bayan nazari a kan wadannan wakoki an yi shari dalla-dalla game da jigo zubi da tsari da kuma salo da sarrafa harshe na wadannan wakoki.
Muna fatan sakamakon wannan bincike da aka yi za a samu wasu manazarta da za su kara fadada bincike game da bain daya shafi wakokin Marigayi Akilu Aliyu domin hakan zai taimaka ga bunkasar rubutaccen adabin Hausa.
Shawarwari:
Dangane da wannan bincike shawara ta farko da za’a bayar it ace, lallai dalibai ya kamata su maida hankali wajen karatu da kuma kokarin ganin sun aiwatar da dukkan aiyukan da aka basu a makaranta odn ta haka ne zasu kasance ma su kwazo a makaranta da kuma samun nasara a karatunsu.
Karin shawara ga `yan`uawa dalibai bat a wuce tunsarwa ba game da muimmancin aikin bincike ba. Ya kamata suke maida hhankali wajen gudanar da wannan aiki. Haka kuma suke kokarin samun muhimmin batu mai amfani wanda za su shawarwari ga `ya`yansu da dalibansu domin hakanne zai taimaka wajen samar da al’umma ta gari.
Kammalawa:
Wannan bincike da aka yi ya takaita ne bias nazarin wasu wakoki guda uku (3) kacal. Marigayi Akilu Aliyu ya rubuta wakoki da dama yana da kyau a samu Karin wasu manazarta su kara buda bincike ko da kuwa a kan wadannan wakoki guda uku ne wadanda akai wannan bincike a kansu. Don Hausawa sun ce “ilmi kogi ne”.
Manazarta:
Littafai:
Muhammad, D. (1976) Fasaha Akiliyya. Zarial; N.N.P.C
Gusau S.M. (1993) Jagoran Nazarin wakar Baka. Kaduna Fishab Medisa service.
Junaidu I. (1989) Ciza Ka Busa. Zaria N.N.P.C.
Akilu A. (1965) Jakadiyar fikiri: Kano N.M.P.P.
Akilu A. (1965) Kanshin Faida: N.M.P.P.
Kundayen Bincike
Satatima I.G. (1999) Taasashin Adabin Baka a Cikin Rubutattun Wakokin Hausa.
Kundin Neman Digiri na Biyu (M.A) B.U.K. Kano.
Muhammad G.Y. da wasu. (2005) Alhaji (Dr) Mamman Shata da
Wakokinsa a Mazubin Nazari.
Kundin Neman Shaidar Malanta ta Kasa (N.C.E) K.S.C.O.E. Kumbotso.
Mukala:
Gidan Dabini A.A. (2004) Dabarun Rubutun Waka.
Wata takarda da Ado Ahmad gidan Dabino ya gabatar a wajen taron karawa juna sani, wanda kungiyar marubita ta nigeira dda hadin gwiwar hukumar dakunan karatu ta jihar kano ta shirya a dakin karatu na murtala Muhammad, kano.
Rataye
Kanshin faida
Ga akilu mai waka,
Dan Aliyu miskini.
Na bara wajen shehi,
Barhama na Tijjani.
In an fadi wane ni,
Mai fargaba ne ni.
Domin kuwa aini,
Ba mai zunu sai ni.
Na muna aiyuka,
Amma cewa ni.
Na fake da Barhama,
Mai san afuwa ne ni.
Ni na fada dai ni,
Ni yanzu a cewa ni.
Niyya da nake din nan,
Mai son Magana ni.
Amma yanzu gausu,
Alfahari rabbani.
Allahu kai ne Allah,
Mai tsarkake zamani
In ar yagurbata,
Karshen dukkan karni.
Bawa daga bayinka,
Zai zammasa buni.
Yau dai ibraimu,
Alfarifu Rabbani.
Gausus samadani,
Wannan dai shi ni.
Alkaulayi inyasi,
Kai tsarkake zamani.
Tun tuntuni na bishi,
Na karfafa imani.
Domin shi ne gausu,
Samadani rabbani.
Yau ba wani sai shehi,
Barama a zamani.
Mai yawan kazanta ne,
Dauda ta dusasheni
Yamma da gabas dinsu,
Duk ba wani sabani.
Faida ma’abocinta,
Barama na Tijjani.
Shi dan bawan Allah.
Ya mamayin zamani.
Aljan da mutanen sa,
Dawwabu da ayawanu.
Dukkan abu ba gefe,
Barhama muke gani.
Kowa kuskura ya baude,
Ya kuskure imani.
Allahu kiyashe mu,
Amin mu fadei harni.
Ni aliyu mai waka,
Dan Aliyu miskini.
Na gaskata Barhama,
Ya zuwa da barhama
ALLAHU RAYAMU KAN ZIKIRI
Fazkurni ubangiji ya fada,
Azkurkum in kuna zikiri.
Washkur kuyi godiya a garan,
Ku ki kafirci ku yi zikiri.
Allahu kira yake a gare-
Mu yace, bayi mu yi zikiri.
Harun Allahu na Annabi,
Sai wanda ya bishi kai zikiri.
Jama’a Allahu ya sa mukula,
Mubi hurunnan muyi zikiri.
Allah rayamu kan zikiri,
Ka kashemu muna cikin zikiri.
Domin kaine hakimu gwani,
Kaine sarki guda wutiri.
Kai ne da gani da ji masani,
Kai ne mai gyara al’amuri.
Mu tattara ko wane zarafi,
Mu barshi a gafen yau da zikiri.
Dukkan lamari nayi bayani,
Kai ne da kyawunsa ya mazari.
Ya Allah taimakemu mudau-
Wama har abada cikin zikiri.
Jama’a muyi tsit saboda mu je,
Ga hairin cikin zikiri
Zan dan gutsira kadan na fada
Cikin falalar zikiri.
Malam kasa kunne ka ji,
Ni ina son ba mu albisiri.
In ar tsanani ya riski mutum,
Zai sauka in yai zikiri.
In fatara ta samu mutum,
Zai yalwata in yayi zikiri.
Yayin da wuya ta riski mutum,
To kar ya sake da yin zikiri.
Ni’ima ta zahiri da fake,
Ta tabbata karkashin zikiri.
In zum yi kiransa ya Ahadun,
Zai ce, labbaika mai zikiri.
Su mum fi wujuhihim,
Gurbin sujjada mutan zikiri.
Da siffofi nasa can a cikin,
Attaura masu yin zikiri.
A zabura akwai sifa tasu ba
Yi wanda suke yawan zikiri.
A cikin injila da akwai.
Sifa tasu masu yin zikiri.
Kur’ani y ace mukula,
Shi kansa ake kira zikiri.
Wato da ganinsu basu ba ne,
Domin hasken cikin zikiri.
Ya mu bayi kiranmu nake,
Mu roki Ubangiji wutiri.
Kunsan Allahu ne ya fada,
Dukkan komai yana zikiri.
Jama’a Allah yasa ku,
Ji ni da kunnan fikira

Leave a comment